Fadar Shugaban Ƙasa ga Gwamnan Bauchi: Ka janye kalaman barazanarka akan Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa ga Gwamnan Bauchi: Ka janye kalaman barazanarka akan Tinubu

A ranar Litinin ne fadar shugaban kasa ta bukaci gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya janye abin da ta kira kalaman nasa na tada hankali kan dokar sake fasalin haraji.

Ya ce furucin Mohammed, "Za mu nuna wa Tinubu launin mu na gaskiya," ba ya nuna matsayin Arewa ko tattaunawa mai ma'ana da ake bukata tsakanin jihohi da Gwamnatin Tarayya.

Mai ba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwar jama’a, Mista Sunday Dare, ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafawa manema labarai a shafin sa na X da safiyar Litinin mai taken ‘RE: Za mu nuna wa Tinubu Launinmu na Gaskiya.

Dare yana mayar da martani ne ga kalaman Mohammed daga ranar Laraba, 25 ga watan Disamba, 2024, yayin bikin Kirsimeti da al’ummar Kirista suka yi a gidan gwamnati da ke Bauchi.

Gwamnan ya yi adawa da manufofin sake fasalin haraji na Tinubu, inda ya kwatanta su a matsayin "masu adawa da arewa" da kuma fifita wani bangare na kasar kawai.

Ya yi gargadin cewa idan aka ci gaba da wadannan tsare-tsare, yankin arewa zai “nuna ainihin launukansa” don mayar da martani. Mohammed ya kuma jaddada cewa irin wadannan sauye-sauye na iya haifar da koma baya ga tattalin arziki da kuma yin barazana ga hadin kan kasa, inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba lamarin tare da daukar wasu tsare-tsare masu amfani.

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce, “Ina rokonsa da ya janye wadannan kalamai na cin karo da juna tare da mayar da hankalinsa wajen tattaunawa mai ma'ana da Gwamnatin Tarayya dangane da duk wata damuwa game da dokar sake fasalin haraji.