Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

 

A kokarin warware rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna  Nyesom Wike na Jihar Rivers. 

Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.
An yi ganawar ne a gidan gwamnatin Rivers dake Asokoro a Abuja a ranar Alhamis. 
Majiyar ta ce da yawa cikin wadanda suka bi Atiku zuwa wurin taron ba su ji dadin yadda Wike ya rika yi wa Atiku magana kan wasu batutuwa da ke janyo rikici a jam'iyyar ba. 
Ya ce dan takarar shugaban kasar ya roki Wike cewa 'yan Najeriya na bukatar PDP ta ci zaben 2023 kuma ya bada dalilin da ya sa ya kamata Wike ya kawo karshen rikicin. 
"Mun kadu kan yadda Wike ya mayar da martani." 
Gwamnan ya tunatar da Atiku kan taronsu na Landan da yarjejeniyar da suka yi. 
Alkawarin da Atiku ya yi na cewa zai yi magana da shugaban jam'iyya na kasa Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus. 
"Alkawarin cewa shi (Atiku) zai tuntube su bayan mako daya amma bai kira ba tun lokacin." 
Jigon ya kuma ce, a cewar Wike, Mambobin BoT sun yarda Ayu ya yi murabus, amma wasu mutane sun zuga shi kada ya tafi. Amma, bayan sauraron Atiku, Wike ya yi alkawarin zai koma wurin mutanensu, su tattauna abin da aka yi a taron kafin ya dauki mataki. 
Kazalika, wata majiya daga bangaren Wike ta ce da wuya a sassanta duba da alkawurra da aka saba musu.
Ya ce an saba masu alkawali yanada wuya su amince da duk abin da za a zo masu da shi a nan gaba.