Gwamnatin Kano za ta shigar da fursunoni cikin shirin inshorar lafiya
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar lafiyarta a jihar domin samar musu da ingantaccen kula da lafiya kyauta yayin da su ke a tsare.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama’a na Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Najeriya reshen Jihar Kano, CSC Musbahu Kofar-Nasarawa, ya sanya wa hannu a yau Litinin a Kano.
Kofar-Nasarawa ya rawaito shugabar Hukumar taimakekeniyar lafiya ta Jihar Kano (KACHMA), Dr. Rahila Aliyu Mukhtar, tana fadin haka yayin ziyarar ta ga Shugaban Hukumar kula da gidajen gyaran hali na jihar, Ado Salisu, a ofishinsa.
Shugabar hukumar ta ce Gwamna Abba Kabir-Yusuf ne ya amince da shigar da fursunonin cikin tsarin inshorar lafiyar domin ba su damar samun kulawa da lafiya kyauta da cikakkiya yayin da suke tsare.
Sannan ta tabbatar wa shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali cewa gwamnatin jihar a shirye take don tallafa wa fursunoni ta fuskar lafiyar jiki yayin da suke tsare.
Ta kuma yi kira ga fursunonin da su kasance suna yi wa Gwamna Kabir-Yusuf addu’a domin ci gaba da samar da romon dimokiradiyya ga kowa da kowa.
managarciya