Abin Da Sauri Haka Za a Kafa Kungiyar Goyon Bayan Tinubu 2027

Abin Da Sauri Haka Za a Kafa Kungiyar Goyon Bayan Tinubu 2027
 

Wasu ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a jam’iyyar APC sun nuna za su goyi bayan Bola Ahmed Tinubu ya zarce. 

A ranar Litinin, Leadership ta rahoto ‘yan siyasar suna cewa za su hakura da burinsu domin Bola Ahmed Tinubu ya samu tazarce. 
Wadannan masu neman mulki a jam’iyyar APC sun kafa kungiya da su ka kira '2023 APC Presidential Aspirants' da za a kaddamar a yau. 
A  yau, 18 ga watan Disamba 2023, za a bude kungiyar a Transcorp Hilton a garin Abuja yayin da wasu su ka fara buga gangar 2027.
Shugaban wannan tafiya shi ne tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yerima kuma wanda ya nemi tikiti a APC a zaben 2023. 
Rahoton ya ce a tafiyar akwai Dr. Nicholas Felix wanda ya yi takara da Bola Tinubu a bana, shi ne ‘yan autan cikin masu neman takarar. 
‘2023 APC Presidential Aspirants’ ta ce za ta fara wannan shiri ne saboda sun hakura da burinsu, sun yi na’am da tafiyar Bola Tinubu. 
A jawabin da kungiyar ta fito, tayi alkawarin taimakawa Mai girma Bola Tinubu a zabe mai zuwa da ake sa ran zai nemi ya zarce. 
Vanguard ta ce za kuma ayi amfani da damar bude kungiyar wajen shirya liyafar karshen shekara domin a goyi bayan gwamnati. Kungiyar nan za tayi uwa da makarbiya wajen ganin an yada manufofin gwamnati mai-ci tare da hada-kai da 'yan Najeriya da ke ketare.