DON NA ƘI AMINCEWA DA SHUGABAN MAJALISA YA YI LALATA DA NI NE DALILIN KIYAYYARSA DA NI---Sanata Natasha
Daga, Jamilu Sani Rarah Sokoto.
Kiyayyarsa Dani Ta fara ne a watan December lokacin da Nake Murnar cika Shekara, Wanda Shima a lokacin yake murnar Cika Shekara (kusan ranar Haihuwar mu daya), dashi Sanata Akpabio
Mun Hadu ne ni da mijina a wani yammaci a gidansa dake akwai ibon In ya rika Hannuna yace, inzo ya Nuna min tsarin gidansa.
Na bishi muna tafe yana Nuna min Shi Kuma mijina yana bin mu daga baya yana waya, har muka zo a wani karamin falo muka zauna.
Sai Sanatan ya dube ni yace min, Shin gidan nan ya burge ki? Na ce masa, Sosai gidan ya tsaru Gwanja shaawa. Anan ya buda Baki yace, min ko zan samu lokaci mu zo nan mu huta ni dake kawai? A lokacin da ya fadi haka mijina yana dan nesa damu. Sai na juya na kalli mijina in gani ko yaji. Shima Shugabana Majalisar da na kalli fuskarsa naga alamar Tsoron Kar azo mijina yaji.
Anan dai muka bar gidan, da dare mijina yayi ta tambaya ta Akan me Sanata yace, min naki gaya masa domin na San Yanda yake daukar Sanata da Muhimmanci Kuma Gashi zaayi bikin murnar Haihuwata bana so na bata farin cikin.
Wannan na daga Cikin dalilan da yasa Sanata ya fara kyara da hantara ta a Majalisa.
managarciya