Ahmad Aliyu ya samu nasarar lashe zaben APC a Sakkwato

Ahmad Aliyu ya samu nasarar lashe zaben APC a Sakkwato
Ahmad Aliyu ya samu nasarar lashe zaben APC a Sakkwato
Tsohon mataimakin gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyar APC a Sakkwato
Ahmad Aliyu ya samu kuri'a dubu daya da tamanin(1080).
Ya kayar da abokan karawarsa su biyar in da Sanata Ibrahim Gobir kuri'a 36, Abubakar Umar Gada bai samu komai ba, Alhaji Yusuf Suleiman ya samu 16, Abubakar Abdullahi ya samu daya, sai Ambasada Faruku Malami Yabo ya samu 27, kuri'un da suka lalace 23.