Dimokaradiyya irin na ƙasashen yamma ba ta kamaci Nijeriya ba – Al-Mustapha
Tsohon babban dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya ce dimokuradiyyar yammacin duniya ba ta kamaci Najeriya ba
A cewarsa, dole ne Najeriya ta samar da tsarin mulki wanda ya dace da manufarta maimakon kwaikwayon na Amurka.
Al-Mustapha, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai bin dimokradiyya a yanzu, ya kuma yi Allah-wadai da masu kira da a yi juyin mulki a kasar, yana mai cewa gwamnatin mulkin soja ba ta zamani ba ce.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance a 2023 ya fadi hakan ne yayin tattaunawa da ‘yan jarida a Abuja a jiya Laraba kan yadda zanga-zangar matsin rayuwa ta rikide ta rikide zuwa tashin hankali a yankin Arewa, inda wasu su ka riƙa daga tutar Russia tare da neman shugaba Bola Tinubu ya sauka daga mulki.
Ya ce duk da cewa wasu ‘yan siyasa ba su gamsu da ra’ayinsa ba, amma shi ya gamsu da hakan.
“Wasu ‘yan siyasa sun zo wurina suka ce, ‘Baka bukatar ka fadi haka a fili, ka bar mu mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu kamar yadda muke, amma ba zan iya zama wani bangare na yaudara ba. Me na ce? Na ce Amurka kasa ce da bakin haure da suka zama ’yan kasa suke da doka da za ta kare su kuma tambayar da na yi ita ce, a Najeriya wanene dan ci-rani ne kuma wanene dan kasa ne?
"Ya za ka yi tsarin mulkin da ya ke baiwa baƙin haure kariya? Kai a Nijeriya ina bakin hauren su ke? Dukkan mu ƴan ƙasa ne," in ji shi.
managarciya