'Yan Najeriya 430,000 su ka samu bizar Burtaniya cikin watanni bakwai

'Yan Najeriya 430,000 su ka samu bizar Burtaniya cikin watanni bakwai

Jakadan Biritaniya a Nijeriya, Dr Richard Montgomery, ya bayyana cewa kawo yanzu gwamnatin Burtaniya ta bada biza ga ƴan Nijeriya akalla 430,000 da ke neman yin karatu da zama a ƙasashen Birtaniya a 2024.

Montgomery ya bayyana hakan ne a wata ganawa da shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, a Abuja a jiya Laraba.

Ya kuma tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa za a samar da isassun matakan tsaro ga ƴan Najeriya mazauna kasashen Birtaniya.

Ya yi nuni da cewa, Masarautar Burtaniya ta kasance mai cikakken tsaro duk da tashe- tashen hankulan da ake fama da su, yana mai nuni da yawan al'ummar kasar.