'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Liman Da Wasu Manoma 2 A Sakkwato

'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Liman Da Wasu Manoma 2 A Sakkwato

 

'Yan bindiga sun kashe mutum uku ciki har da babban limamen kauyen Gangara a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.

Babban limamen wanda aka fi sani da Liman Na-Kimba an kashe shi a ranar Laraba a lokacin da yake dawowa daga Sakkwato bayan ya karbo fanshonsa. 
Wata majiya ta ce motar da ta dauko su ta yi kuren hanya ta shiga sansanin 'yan bindigar a kauyen Adamawa in da aka buda masu wuta.
"daya daga cikin harsashen da aka harbe su ya samu Liman ya kashe shi" a cewar majiyar.
Hakama 'yan bindigar sun kashe manoma biyu a kauyen Dunkawa duka a  Gatawa kwana uku da Suka wuce.
Maharan sun yi garkuwa da wasu manoma 6 a lokacin da suke aiki a gona.
Shugaban 'yan banga a Sabon Birni Musa Muhammad ya tabbatar da lamarin ya ce an yi janazar margayan.