Gwamnatin tarayya ta gurfanar da ƴan kirifto 4 a gaban kotu
Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar wasu ƴan Kirifto guda hudu bisa zargin lefin kasuwancin siyar da Dalar Amurka ba tare da lasisi ba.
Mutanen da ake karar sun haɗa da: Ejiogu A. Chinedu da Nnamadi F. Okereke da Oty Ugochukwu Stanley da Chukwuebebuka F. Ogumba tare da wasu kamfanoni.
A takardar ƙarar da aka shigar, gwamnatin ta buƙaci babbar kotun tarayya dake Abuja ta hukunta waɗanda ake karar bisa zargin saɓa dokar bankuna da fannin hada hadar kudi ta 2020.
NairaMetric, tunda farko ta rawaito cewa, hukumar EFCC ta samu umarnin kotu a ranar 4 ga watan Satumba na 2024 domin rufe asusun ajiya na banki mai dauke da Naira Miliyan 548.6 da ake zargin suna da alaka da ƴan Kiripto.
managarciya