Fitacciyar mawakiyar addinin Musulunci, Ruqayya Gawat ta rasu
Fitacciyar mawakiyar nan ta addinin Musulunci, Rukayat Gawat Oyefeso ta rasu.
Mawakiyar ta yi shura da wakokin ta a cikin al'ummar Musulmai a kudancin Nijeriya.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa fitaccen Malamin nan na Ilori Alfa Aribidesi At-Tawdeeh ne ya bayyana rasuwar ta a shafin sa na Facebook a safiyar yau Talata.
Har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan rasuwar ta ba.
Rasuwar mawakiyar ta haifar da jimami ga masoyan ta inda ake ta yada labarin rasuwar.