Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani 

Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani 

Babban bankin Najeriya, CBN ta bi dukkan matakan da suka dace wurin sabunta takardun naira uku da zai yi, Daily Trust ta rahoto. Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ya sanar da hakan yayin martani ga Ministan kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed, wacce tace ma’aikatar ta bata da masaniya kan sabon tsarin.

A yayin da ta bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai a ranar Juma’a, ministan ta soki lamarin wanda tace bai dace a wannan lokacin ba. 
Amma Nwanisobi ya bayyana mamakinsa kan ikirarin ministan inda yace CBN ma’aikata ce kafaffiya kuma ta aikewa Buhari wasika kan cewa zata sauya wasu takardun Naira wanda ya amince da hakan. 
Yayi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan sauya kudaden inda yace dukkan ‘yan Najeriya zai amfana tare da jaddada cewa wasu mutane sun boye kudade masu yawa ba a ma’adanar bankunan kasuwanci ba. Wannan yayin yace bai dace a bar shi tsakankanin ‘yan Najeriya ba da basu yi wa kasar fatan alheri.