Yadda wata daliba ta gaiyato ƴan daba su ka ƙaddamar wa wani malamin kwaleji a Kano

Yadda wata daliba ta gaiyato ƴan daba su ka ƙaddamar wa wani malamin kwaleji a Kano
Wata daliba a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, wacce aka dakata sunan ta ba, ta gaiyato ƴan daba da suka kutsa kai makarantar su ka kuma sassari wani malami, Aliyu Hamza Abdullahi, a ranar Talata, 14 ga Janairu, 2025.
Malamin, wanda shi ne jami'in jarabawa na sashen, rahotanni sun ce an kai masa hari ne bisa jagorancin saurayin dalibar.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa lamarin ya faru ne sakamakon rashin gamsuwa da dalibar ta yi da kwas din da aka ambata lokacin da ta nemi gurbin karatu a kwalejin.
Jaridar ta rawaito cewa lokacin da dalibar ta yi kokarin canja kwas din, sai aka shaida mata cewa hakan ba zai yiwu ba sakamakon wanda take so ta sauya, makin ta na jarrabawa bai kai ba.
Jami’in hulda da jama’a na Kwalejin, Auwal Ismail Bagwai, ya tabbatar da afkuwar harin yayin taron manema labarai a Kano a jiya Juma’a, ya bayyana cewa, “harin ya faru ne yayin da malamin ke gudanar da aiki a ofishinsa da misalin karfe 2 na rana a ranar Talata. Dalibar ta shiga ofishin tare da saurayinta, inda su ka bayyana cewa malamin ne ya hana ta cimma burinta. Nan take saurayin ya fito da adda ya sassari malamin.”
Bagwai ya kara da cewa, “malamin ya samu raunuka a hannayen sa yayin da ya ke kokarin kare kansa. Dalibai da ke cikin ofishin suka shiga tsakani, wanda ya sa wadanda suka kai harin suka tsere.”
"Bayan harin, an garzaya da malamin zuwa asibiti don kula da lafiyar sa. Daga nan kuma jami'an tsaro na makarantar suka je unguwar Dorayi, inda dalibar ke zaune, domin cafke ta da saurayin ta.
"Amma lokacin da suka isa, dalibar ta shige gida, sannan gungun 'yan daba suka fito dauke da makamai suka kai hari kan jami'an tsaron.
Bagwai ya tabbatar da cewa, “jami'an tsaro na ci gaba da bincike kan lamarin, yayin da malamin da aka kai wa hari ke samun kulawa a asibiti.”