Zaben 2023: Rundunar  NSCDC da 'Yan Jarida sunyi taron  hadin gyuwa a Zamfara

Zaben 2023: Rundunar  NSCDC da 'Yan Jarida sunyi taron  hadin gyuwa a Zamfara

Hussaini Ibrahim
Gusau.

 A ci gaba da shirye-shiryen da hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya ta gudanar a jihar Zamfara, Kwamandan jihar, karkashin jagorancin Kwamanda Muhammad Bello Muazu ya shirya wani taron hadin gyuwa da kungiyar (NUJ) ta  ‘yan jarida a jihar Zamfara ,zasu taka a rahoton zabe a babban zaben 2023. da za'a gudanar da shi wannnan wata da wata me zuwa.

Taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reagent jihar Zamfara, da rundunar ta shirya shi ne domin lalubo hanyoyin gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana.

 Kwamandan Muhammad Bello Muazu ya shaidawa manema labarai cewa,sune gishirin babbar miyar da za'ayi a zabe mai zuwa ,dan haka sune idanun alumm wajan sauraran rahotannin gaskiya da alumma zata dogara da su.dan haka kuni sanci labaran karya da shaci fadi dan samun nasarar zaben.inji Kwamandan"

"Don haka kwamandan MB Muazu ya yi kira ga malaman alƙalan zabe da su kasance masu gaskiya da adalci da kuma sahihanci a cikin rahotannin da suka shafi harkokin zaɓe domin samar sahihin zaɓe na gaskiya.

Kwamanda Muhammad Bello Muazu ya kuma bukaci ‘yan jarida da su hada kai da jami’an tsaro wajen yaki da duk wani abu ko bayanan da ke kawo barazana ga gudanar da babban zaben kasar cikin sauki.

Anasa jawabin Kwamaret Ibrahim Musa Maizeri shugaban kungiyar ‘yan jarida na Kasa reshen jihar Zamfara, ya yabawa shirin , Rundunar farin kayan karkashin jagorancin Kwamanda MB Muazu bisa shirya irin wannan taron. ya ce wannan shi ne irinsa na farko a tarihin jihar Zamfara.

Kwamared Maizeri ya yi alkawarin ba Rundunar  goyon baya ba tare da bata lokaci ba domin samun nasarar babban zaben 2023.

Don haka ya tabbatar wa Kwamandan cewa, a matsayinsu na hudu a harkokin mulki, a shirye suke su magance matsalar labaran karya wadanda galibin masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani ne ke yada su.

Don haka ‘yan jaridan a shirye suke su bayar da rahotannin gaskiya da kuma ingantattun labarai domin dakile tashe-tashen hankula na siyasa a lokacin babban zaben da ya kara da cewa.

Haka kuma, sauran tsofaffin Ma'aikatan  aikin jarida sun bayar da gudunmawa mai ma’ana wadanda ke da muhimmanci a dan ganin sunyi amfani su lokutan zabe.