'Yan Bindiga Sun Yanka Limami Tare Da Kashe Mutum 8 A Zamfara
Bayanan dake zuwa mana sun nuna cewar, mayakan da suka isa kauyen Tungan Ruwa akan babura, sun dinga harbi kan mai uwa-da-wabi, kafin su isa gidan limamin garin. Wani shaidar gani da ido ya shaida mana cewar a gaban mutanen kauyen ‘Yan bindigar suka yanka limamin, yayin da suka kuma harbe wasu mutane 8 har lahira. Karamar hukumar Anka na daya daga cikin yankunan Jihar Zamfara da suke fama da hare haren ‘Yan bindiga, wadanda suka yi sanadiyar kashe daruruwan mutane da kuma tilastawa wasu da dama barin kauyuka da garuruwan su. Yanzu haka mazauna wannan karamar hukumar da dama na samun mafaka a kananan hukumomin Maru da kuma Talatar Mafara.
'Yan Bindiga Sun Yanka Limami Tare Da Kashe Mutum 8 A Zamfara
'Yan bindiga sun kai hari a kauyen Tungar Ruwa a karamar hukumar Anka jihar Zamfara bayan sun yanka limamen gari suka kashe mutum takwas anan take.
Rahotanni sun ce a daren laraba ‘Yan bindigar suka kai harin, amma saboda katse layukan sadarwa a sassan jihar, ba’a samu cikakken bayani akan yadda lamarin ya faru ba.
Bayanan dake zuwa mana sun nuna cewar, mayakan da suka isa kauyen Tungan Ruwa akan babura, sun dinga harbi kan mai uwa-da-wabi, kafin su isa gidan limamin garin.
Wani shaidar gani da ido ya shaida mana cewar a gaban mutanen kauyen ‘Yan bindigar suka yanka limamin, yayin da suka kuma harbe wasu mutane 8 har lahira.
Karamar hukumar Anka na daya daga cikin yankunan Jihar Zamfara da suke fama da hare haren ‘Yan bindiga, wadanda suka yi sanadiyar kashe daruruwan mutane da kuma tilastawa wasu da dama barin kauyuka da garuruwan su.
Yanzu haka mazauna wannan karamar hukumar da dama na samun mafaka a kananan hukumomin Maru da kuma Talatar Mafara.
A cikin wannan makon ‘Yan bindigar sun yiwa tawagar ‘Yan Sandan kwantar da tarzoma kwantan bauna a Jihar inda suka kasha guda 7 daga cikin su.
Mahara suna ci gaba da kai hari na mai kan uwa da wabi a yankunan Sakkwato da Zamfara
managarciya