Sojoji sun kashe dan Turji sun lalata maboyar makamansa a Zamfara

Sojoji sun kashe dan Turji sun lalata maboyar makamansa a Zamfara
 

Sojojin Nijeriya sun kashe dan Bello Turji shugaban 'yan ta'adda a maboyarsa a Zamfara.

Majiya ta tabbatar da rundunar soja Fansar yamma ce takai harin ta sama a garin Fakai in da 'yan uwan Turjin suke a karamar hukumar Shinkafi jihar Zamfara.

Bayanan sirrin sun tabbatar da Turji ya rasa wasu iyalansa da makusantansa, har ya kira wasu shugabannin 'yan ta'adda bakwai domin agaza masa, amma ba wani da ya zo.

Daga cikin dabar da sojojin za su kaiwa hari sun hada da Zangon Dan Gwandi da Zangon Tsaika da Zangon Kagara, makarantar da turji ya mayar ma'ajiyar makamansa bayani ya fito sojoji sun kone makarantar don kare kai masu hari daga makarantar.

Farmakin na karkashin runduna ta musamman wadda babban kwamada(GOC) ke ba ta goyon baya.

Alhaji Bashir Altine Guyawa ya tabbatar da kai farmakin ga maboyar Turji a wani rubutu da ya wallafa a fajinsa na facebook.