ANA BARIN HALAL..:Fita Ta Bakwai
ANA BARIN HALAL..:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*PAGE* 7
Washe garin sallah iyayen Aliyu suka zo wurin Abbah na neman ison Aliyu ya gani yana so, kuma da neman iznin ya fara zuwa zance, cikin mutunci Abba ya karɓe su, kuma ya bada daman yazo, amma da sharaɗin baya son dogon nema, idan mun sasanta kanmu baya so abu ya ɗauki lokaci, kuma baya son yawan zuwa zance, haka taron ya watse kowa fuskan shi cike da farin ciki, amma ni kuma takaici kaman zai kashe ni, baya ma da naga habiba ta saka hannu biyu tayi tagumi, duk sai naji abun bai mun ba, muna shigowa parlor nida habiba muka haɗu da mamie, fuskan ta cike da fushi ta kalle ni, babu kara tace, "sannu madam Aysha, wato an baki suratul yusuf an haɗa miki da surkulle sai murna kike kin samu mai so ko? Tou ayi dai mugani, amma insha Allahu bazaki riga habiba auruwa ba kam a gidan nan, kai hattah Raliya ma sai kin rakata, don ba rako mata duniya nayi ba ballantana na zura ido".......
"lallai ko zai tabbata kin rako mata duniya mushirikiya kawai, ke kam ban san ranan da zakiji tsoron Allah a zuciyar ki ba, gani kike duk surkullen da kikeyi wani ma haka yakeyi"? Cewar Aunty Rakiya da shigowan ta kenan gidan, tsaki mamie tayi ta wuce ta bar wurin batare da ta tanka wa Aunty Rakiya ba.
Ita ko Aunty Rakiya haka takama masifah har ta wuce ɗakin ummin mu, rai a ɓace takama masifa akan shirun ummi yayi yawa, sannan ta ƙara addu'a fah, don zuciyar mamie babu Allah a ciki, murmushi ummi tayi tace, "banda abunki Rakiya mamin su ta isa ta hana abun da Allah yayi nufi? Kuma ni kullum addu'a na akansu yake, babu dare babu rana, kuma insha Allahu khairan, ni damuwa na ma da ita Ayshan kaman yaron bai mata ba, gashi kuma mahaifiyar tana son abun, ni har kunya nakeji wlh".
Wuri Aunty Rakiya ta nema ta zauna, "tou idan Aysha bata so ae baza a mata dole ba, kawai addu'a zamu dage, idan babu alkhairi Allah ya kawo mata wanda yafi alkhairi, amma babu dole babu kuma kunya", amma dai abun bahaka naso ba, don ni banga aibin yaron ba, cewar ummi,
Ita ko yarinya taga aibu, kuma babu mai takura mata sai abun da taso" Aunty Rakiya ta faɗa, ita dai ummi murmushi tayi ta sake zancen ta koma wani chafter daban.
Ranan sallah na uku Yayah Aliyu yazo gidan mu, parlor Hjy ummah habiba ta kaishi, bayan sun gaisa ta kai mishi abun sha da cake ɗin da mukayi na sallah da cincin sai naje, hiran dai dani kam babu armashi, amma shi ds habiba kaman sun shekara da sanin juna, nidai ban da ehh da a'a babu abinda yake ji daga gareni, ganin haka sai ya maida hankalin shi kan habiba yana ta bata shawara akan karatun ta, tunda shima computer science yake koyarwa, nidai gaba ɗaya hiran ba wani ɗaɗani da ƙasa yayi ba, saboda nakasa jin wani abu akanshi, sai dai ban wani nuna mishi sosai a fuska ba, babu daɗewa sai ga Raliya ta shigo, ko gaishe shi batayi ba kanta tsaye ta kalli habiba tace, "kizo mamie na nemanki" daga nan ta juya ta fita a parlon, dukkan mu kallo muka bita da shi cike da jin kunyan abinda tayi, shikuma da yake ba mai damuwa bane idon shi kawai ya mayar kan habiba yace, "tou Aunty habiba godiya nake, amma a ƙara riƙe mun wuta fah" ya faɗa cike da zolaya, itama dariyan tayi tace, "baka da matsalah sai dai ka nemi wani abun kuma daban" daga haka ta fita, shi kuma ya maido da hankalin shi na, "ina muka tsaya ne princess?"
Ɗago kai nayi na dube shi, muryah cike da rauni nace "babu komai",
Zura mun ido yayi har sai da naji nauyin idon shi akaina ya mun yawa, sai dube -dube nake tayi akan wayana, ba tare da nasan me nake ganiba, duk a takure nake, ganin haka yace, "tou princess nidai zan wuce sai munyi waya, fatan babu wani abu ko"?
Cikin gaggawa na amsa mishi da babu komai na gode," ina miƙewa kaman an ɗana mun abu, murmushi yayi yace, "tou a mun rakiya mana".
Zaro ido nayi ina kallun shi nace, "Rakiya kuma? ae za'a ganni, nidai kawai.... " sai kuma nayi shiru ina maida kaina ƙasa saboda irin kallon daya ƙureni da shi, bai wani ja ba ya juya ya fita yana cewa, "baki da saƙo wurin mummy"? Da sauri nace a gaisheta.
Bayan ya fita hjy ummah ta fito tana ya mutsa fuska tace, "ashe ke sokuwa ce ban sani ba? Wannan wani irin zance ne babu armashi? Sai dai ƴar'uwarki ce bakin ki? Tou a kul kada nasake ji ko ganin wannan ƙauyancin, don ko mutanen da iya kachi".
Tura baki nayi gaba ban bata amsa ba na fiche a parlon.
Wasa-wasa shaƙuwa tsakanin Aliyu da habiba sai yafi ƙarfi, wani lokacin ma idan ya ƙira waya na sai dai hiran ya koma da habiba, zuwa ɗari kuma hiran da ita yafi armashi, nidai nawa ido da binsu da kallo, a haka mukayi wata uku tare da shi, lokacin kuma mahajjata sun dawo makkah, da yake mummy taje, sai ga kaya na fitan tunani an kawo mun tsara ba, ranan ina wuta mamie ta jefah ni a ciki, haka tayi ta banbami tana cewa ummi ta rufe taurarin farin jinin ƴarta, don shigan habiba side ɗin mu tasan ba ƙaramin illah akeyi wa ƴarta ba, amma a zuba da ita insha Allahu sai ummin tayi kuka, kuma daga yau ta shiga tsakanin habiba da ni, idan ba mugunta ba ummi ma taja kunne na da ƴarta, ko kula ta kanta ummi batayi ba, sai mamah ne ta fito ta watse ta iya son ranta ta kuma ce ta jira dawowan Abba da hukuncin da za'a ɗauka, don wannan mummunan fatan da takeyi idan ita ummi bata ɗauka ba ita mamah zata ɗauka, duk abunda akeyi Raliya tana tsaye sai bina da kallon banza ta keyi, ƙasa-ƙasa tana zuga mamie, haka dai akaita rikici.
Bayan dawowan Abba mamah ta tasu da maganan agaban kowa, kuma ta rantse idan Abba bai dakatar da matan shi ba ita zata dakatar, cike da banbami take magana, ita kuma mamie ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya tana wani jijjigawa, a ƙarshe dai Abba yayi gyaran muryah yace,
"don Allah ku saurara mun, yanzu ko a tunanin ku akwai asiri? Kun ma yadda da akwai kenan? Tou ni ban yadda akwai ba, amma duk da haka zan tsawatar da irin wannnan muggan fatan da akeyi wa ƴaƴa na", ya juya yana duban mamie, "don Allah mamin su bana son tashin hankali, shin Aysha ke ba ƴarki bace? Tou me yasa zakina jifanta da munanan kalamai? Don Allah ku zama ɗaya kowa yabar maganan nan bana son ya fita ma, kuma da yau bana son a dinga shiga tsakanin ƴaƴa nah, a barsu suyi zumuncin su bana son a raba mun kan ƴaƴa a damuwan ku na banza da wofi", sannan ya maida kanshi kan ummi yace, "ummin su don Allah bana son abubuwa na chanfi a gida na, wannan maganan ya fito ne saboda mamin su bata da haƙuri ko kaɗan shiyasa idan ranta ya ɓaci sai tayita magana babu kan gado, amma bawai nufin ta ta cutar da wani bane, fatan kowa ya gane kuma maganan zata tsaya a haka"?
Murmushi ummi nah tayi ta kau da kanta gefe tace, " dama ni ka taɓa ganin na taɓa zargin wani a rayuwata? Nayi imani fah da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, kuma ban saka zuciyata akan wani ya isa ya cutar dani ko yarah na ba, don na dogara da Allah, kuma nasan zai isar mun akan komai".
Baki a buɗe mamah take bin Abba da ummi da kallo, chan tace "tou haka zancen yake kenan ko? Kai a irin adalcin ka kenan iya abun da zaka ce kenan? Tou Allah ya mana jagora", sannan ta maida kanta kan ummi tace, "ke kuma baiwar Allah ya isar miki yadda kika ce, kuma Allah ya tsare ki da yaranki daga sharrin mai sharri, amma mukan mun sha tabara mun sha lahaula, duk sharrin mai sharri haka zai barmu," ta faɗa taa barin wurin tana faɗin ita ta gajji da ganin kayan ɓacin rai.
Bayan kwana biyu da mamie ta hana habiba shigowa side ɗin mu, sai zaman mu ya koma chan wurin hajiya ummah, amma kuma abinda na lura sai Raliya ma ta maida zamanta chan, amma duk da zamanta a wajen baya wani lasting sbd abu kaɗan zasu kanchale da Hafsy sai kuma hjy ummah ta fatattake su, nida habiba kuma ganin an koresu sai muyita dariyan su, a ranan kuma habiba ke gaya mun raliya ae ƴar aike ne, gulma take kaiwa mamie, nidai dariya nayi nace, "zata shiryu ae, yarinta ne yake damunta".
Gaba ɗaya sai zaman mu da kwanan mu ya koma chan, saboda mai aikin hjy umma da tayi tafiya, gashi zazzaɓi ya sako hjyr a gaba, sai Abba yace mu koma chan gaba ɗaya muna ɗebe mata kewa, mamie babu yadda ta iya sbd lokacin data so ta dakatar da habiba har cikin gida hajiya ummah ta shiga ta watse ta kuma ta kafa mata kyakkyawan worning.
A hankali na lura Aliyu ya janye ƙirana a waya, sai dai naji shi suna hira da habiba, duk da dai ba hiran soyayyah bane sukeyi, amma duk sai naji jikina yayi sanyi, sai dai bance komai ba, don ni idan ka cire ummi na duk duniya babu abinda nake so irin habiba.
Habiba ta matsa mana ranan friday muje gidan yayah mohd mu wuni wa Aunty Bintu, ban ƙi mata ba muka shiryah mukaje, gashi lokacin da mukaje fatima sister Aunty Bintu tazo mata hutu saboda Aunty Bintu cikinta yayi girma, haihuwa yau ko gobe, sbd ma ta daɗe bata samu haihuwan ba, murna wurin Fatima kaman yayah sbd ita dai son mu takeyi.
Zuwa la'asar sai naga habiba tana amsa wayan Aliyu, bayan sun gama sai ta juyo cike da farin cike tana duban mu tace, "sisto Yayah Aliyu yazo, mu shigo da shi parlor ko"? Ido na zuba mata kaman bazan ce komai ba, sai chan kuma nayi wani tunani, fuska na cike da murmushi nace "sisto tunda yazo ku gaisa ne kije kawai waje ki same shi mana".
Babu ɓata lokaci da magana na ta ja gyalen ta tayi hanyar waje tana faɗin "sisto ki fito tou ku gaisa, bari naje, yace zai kawo mun wani mini computer ne da yayi order shi ya iso, shine zai kawo mun nawa", daga nan tayi hanyar waje cike da sauri.
Zuciya nane ya yanke a lokacin *Aunty nice*, saboda sai na rasa dalilin da naji hankali na ya tashi, kuma kaman alaman kaman naji kishin yayah akayi tsakanin su yakai haka da ƴar'uwata? Amma banja ba sai na ture abun a raina, na maida hankali na kan Aunty Bintu da take mun tambayan bawai saurayina Aliyu bane yazo? Tou meyasa ni ban fita ba sai habiba? Ban iya nace mata komai ba, sai murmushi da na bita da shi, amma *Aunty nice* haka kawai naji zuciyana yana wani irin ɓaci, sai dai dana tuna habiba sister nane sai ture abun a raina.
Daga nan naga Aysha ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wani murmushi marar armashi, har zuwa wani lokaci kaman bazata sake cewa komai ba, sai kuma ta ɗago ta dube ni fuskanta cike da murmushi tace, "*Aunty nice* ina son habiba komai na mallaka zan iya sadaukar mata, amma shaiɗan sai ya fara rinjayar zuciyata naji kaman Aliyu fah ya dace da ni, kuma ina jin wani iri a zuciyata kaman fargaban kada na rasa shi.
*AUNTY NICE*
managarciya