Shugaban APC Na Kasa, El-Rufai da Wasu Gwamnoni 2 Sun Gana da Malami Kan Canja Naira

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gana da Antoni Janar na ƙasa (AGF) kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami, yau Litinin 20 ga watan Fabrairu, 2023.

Vanguard ta ce gwamnonin APC uku da suka kai ƙarar FG gaban Kotun koli sun halarci ganawar wacce ta gudana a babban Sakatariyar APC ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja. 
Gwamnonin da suka halarci taron su ne, Malam Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna, Yahaya Bello na Kogi da kuma Bello Matawalle na jihar Zamfara.
Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gana da Antoni Janar na ƙasa (AGF) kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami, yau Litinin 20 ga watan Fabrairu, 2023. 
 Vanguard ta ce gwamnonin APC uku da suka kai ƙarar FG gaban Kotun koli sun halarci ganawar wacce ta gudana a babban Sakatariyar APC ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja. 
Taron wanda ya shafe kusan awa ɗaya na zuwa ne awanni 48 gabanin ci gaba da sauraron shari'a kan sauya fasalin naira da CBN ya tsiro da shi a gaban Kotun koli ranar Laraba mai zuwa.