Jam'iyar PDP reshen jihar Sakkwato ta tausayawa ma'aikatan jihar Sakkwato da malaman furamare ganin yadda lamarin albashi ya fara tabarbarewa a jiha tun watan Junairu da aka soma biyan sabon albashi na dubu 70.
A wani bayani da sakataren yada labarai na jam'iyar Hassan Sahabi Sanyinnawal ya rabawa manema labarai a Laraba ya ce dole ne mu tausaya da nuna kulawa ga ma'aikatan gwamnatin jiha kan halin da suka shiga wanda ya faru sakamakon gazawar Gwamnatin jiha ga biyan albashi kan kari a kowane wata.
Hassan Sahabi ya ce "wannan abin takaici ne tun sanda gwamnatin APC ta yi yunkurin fara biyan karin albashi da kasa ta amince da shi aka rika samun tsaiko wurin biyan albashi sai akai tsakiyar wata ko wani wata sannan a biya, a hakan wasu za su bi bashin watan da ya gabata.
"PDP ta kadu sosai ganin yadda matsalar albashi ta mamaye gwamnatin Sakkwato duk da kudin da gwamnatin tarayya ke bayarwa a duk wata, babu wani babban aiki na a zo a gani.
"Wannan kasawar ta gwamnatin Ahmad Aliyu na biyan albashin Fabrairu har cikin watan Maris da aka soma azumin Ramadan a cikin tarihin Sakkwato shi ne farko, lamarin abin tir ne a kasa biyan da yawan ma'aikata albashi a lokacin da Azumi ya yi rabi."
Sanyinlawal ya nemi gwamnatin ta daina wannan halin na yaudarar mutanen Sakkwato a cika alkawarin da aka dauka a lokacin yekuwar neman zabe.