Mai baiwa Gwamnan Sakkwato shawara kan harkokin matasa Honarabul Buhari Bello Sahabi Wanda aka fi sani da Buhari Na-Malam ya yi murabus daga mukaminsa a cikin wata takarda da ya aikawa gwamnan jiha Dakta Ahmad Aliyu Sokoto a ranar Laraba.
Honarabul Buhari Bello ya tabbatarwa wakilinmu shi ne ya rubuta takardar ya ajiye mukamin ne bayan ya kammala tuntubar dangi da abokansa da magoya bayansa da Kuma abokan huldar siyasa, sun cimma matsayar ya ajiye mukamin Mai baiwa gwamna shawara na musamman.
Ya ce ajewar ta zama dole ta la’akari da abin da ke faruwa in da gwamnati ke kokarin danne shi da magoya bayansa, “kan haka na ajiye mukamin cikin girmamawa, na gode da damar da Gwamna ya bani na ba da tawa gudunmuwa” a cewarsa.





