Atiku Ya Ragargaji Tinubu Kan Dawo da Tallafin Man Fetur a Ɓoye 

Atiku Ya Ragargaji Tinubu Kan Dawo da Tallafin Man Fetur a Ɓoye 

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki Tinubu kan yadda yake tafiyar da mulkin Najeriya. Atiku Abubakar ya bayyana cewa akwai tarin matsaloli da suka dabaibaye tattalin arzikin kasar da Bola Tinubu ya ki bayyanawa. 

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya ce cikin abubuwan da Tinubu ya ki bayyanawa akwai dawo da tallafin mai a sirrance.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa tun kwanaki ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya fito ya bayyanawa yan Najeriya yadda ake ciki bayan ya cire tallafin man fetur. Ya ce akwai bukatar yan Najeriya su san ina kudaden tallafin suka shiga kuma wane cigaba aka samu bayan cire tallafin amma abin ya gagara. 
Atiku Abubakar ya ce ana cikin bukatar sanin kudin da gwamnati ta tara bayan cire tallafi sai aka ji kudin tallafin da gwamnati ke kashewa ya karu.