Shugaban NNPC Ya Sanar Da Lokacin Da Nijeriya Za Ta Bar Sawo Mai Daga Kasashen Waje

Shugaban NNPC Ya Sanar Da Lokacin Da Nijeriya Za Ta Bar Sawo Mai Daga Kasashen Waje

 

Shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya ce Najeriya za ta dena siyo man fetur daga kasashen waje lokacin da matatar Dangote ta fara aiki zuwa tsakiyar shekarar 2023. 

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wurin taron da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya karo na 49 a Villa, Abuja, The Cable ta rahoto.
Kyari, ya ce za a samu karin man fetur da ake samarwa saboda sabon fasaha da ake amfani da shi, yana mai cewa hakan zai faru a tsakiyar 2023, Daily Trust ta rahoto. 
"Man da za a rika samu daga matatan Dangote da wasu kananan matatun mai na jihohi zai sa a dena siyo man fetur daga kasashen waje. 
"Ko da dukkan matatun mu hudu suna aiki a matakin 90% da aka kafa su. Litan man fetur miliyan 18 kawai za su iya samarwa. Hakan na nufin ko da dukkansu na aiki yau, akwai bukatar a siyo mai daga waje." 
"Man da za a rika samu daga matatan Dangote da wasu kananan matatun mai na jihohi zai sa a dena siyo man fetur daga kasashen waje. 
"Ko da dukkan matatun mu hudu suna aiki a matakin 90% da aka kafa su. Litan man fetur miliyan 18 kawai za su iya samarwa. 
Hakan na nufin ko da dukkansu na aiki yau, akwai bukatar a siyo mai daga waje." 
Ya cigaba da cewa NNPC ce ke da hannun jari kashi 20 cikin 100 a Matatan Dangote don haka ita ce za a fara yi wa tayin fetur din, sai ta ce bata so za a kai kasuwa. 
Kyari ya kara da cewa Matatan na Dangote za ta fara aiki a tsakiyar shekara mai zuwa, yana mai cewa za ta iya samar da lita miliyan 50 na man fetur wato PMS. 
"Idan aka hada wannan da kuma dawo da matatun man mu na kasa zai sa babu bukatar a rika siyo man fetur daga kasashen waje. 
Ba za ka ga ana shigo da wani abu daga kasar waje ba a shekara mai zuwa."