Ango Ya Rasa  Ransa  Yayin Daukar Hotunan Aure Tare Da Amaryarsa

Ango Ya Rasa  Ransa  Yayin Daukar Hotunan Aure Tare Da Amaryarsa

Wani mai shirin zama ango ya mutu bayan tsawa ta fada masa a yayin daukar hotunan kafin aure tare da amaryarsa a wani shahararren wajen shakatawa a kasar China. 

Mummunan al’amarin ya afku ne a tsaunin Jade na kasar China da ke lardin Yunnan a makon jiya. 
An yi gaggawan kwasar mutumin mai suna Ruan zuwa asibiti inda aka tabbatar da ya rasu, jaridar South China Morning Post ta rahoto. 
Kafin tsawar ta saukar masa, hukumomin kasar China sun yi gargadi game da yanayi mai launin dorawa, wanda shine na uku wajen girma a tsarin yanayin kasar, shafin LIB ya rahoto. 
 
Duk da tsawar da aka ta yi, masu shirin zama ma’auratan sun ci gaba da shirinsu na zuwa daukar hotunan.
 An gano yadda tawagar ceto dauke da gawar mutumin kan gadon daukar marasa lafiya a cikin ruwan sama tsamo-tsamo.