APC Ta Rasa Ɗaya Daga Cikin  Shugabaninta a Sakkwato

APC Ta Rasa Ɗaya Daga Cikin  Shugabaninta a Sakkwato

Jam'iyar APC ta rasa ɗaya daga cikin shugabaninta a Sakkwato in da ya koma PDP.
Tsohon Sakataren jam'iyar Alhaji Aminu Bello da aka fi sani da ACY ya sauya sheƙar ne a jiya Jumu'a a hidikwatar jam'iyar PDP a birnin Sakkwato.

ACY yana cikin makusantan tsohon gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sai gashi ya bayyana sauya jam'iyarsa kan wani dalili da ba a bayyana ba.

Shugaban PDP a jiha ne Bello Aliyu Goronyo da Muntari Maigona suka karbi jigon tare da yi masa alƙawalin aiki da shi ba bambanci.