Rikicin APC:Ministan Shari'a Ya Goyi Bayan Mainasara Sani Ne Shugaban APC A Sakkwato

Rikicin APC:Ministan Shari'a Ya Goyi Bayan Mainasara Sani Ne Shugaban APC A Sakkwato

Ministan shari'a Abubakar Malami ya goyi bayan Mainasara Abubakar Sani a matsayin sahihin shugaban jam'iyar APC a Sakkwato.
Malami ya faɗi haka a wurin taron rabon kayan tallafi da dan majalisar waƙillai Abdullahi Balarabe Salame ya raba ga mazabarsa ƙananan hukumomin Gwadabawa da Illela.
APC Sakkwato ta faɗa cikin rikici in da aka samu shigabannin jam'iyya biyu da kowane ke ganin shi ne halastaccen shugaba.
A ɓangare ɗaya masu biyayya ga Sanata Wamakko sai ɗayan ɓangaren dake ƙarƙashin Sanata Abubakar Gada maganar tana gaban kotu.
Malami a wurin taron ya ce zaɓaɓɓen shugaba a Sakkwato wanda kotu ta tabbatar shi ne Mainasara Sani.
Isah Sadik Achuda da yake mayar da martani ya ce Malami ya haɗa kai da PDP a Sakkwato don ya tarwatsa APC ya yi kira gare shi da ya tafi ya magance rikicin jiharsa ta Kebbi kamin ya zo ya kawo matsala a Sakkwato.
"mutumin da ya kasa cin rumfarsa a zaɓen ƙananan hukumomi har shi ke jefa kansa ga abin da mutane suka zaɓa, mu ne zaɓaɓɓin shugabanni a jiha."
"muna tare da sanatoci biyu da 'yan majalisar waƙillai shida da 'yan majalaisar dokoki 13 duka suna tare da mu."