Annoba: Baƙuwar Cuta Ta Ɓulla a Sakkwato, Ta Kashe Bayin Allah

Annoba: Baƙuwar Cuta Ta Ɓulla a Sakkwato, Ta Kashe Bayin Allah

 

Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta NCDC ta tabbatar da ɓullar wata baƙuwar cuta a jihar Sokoto. 

Hukumar ta ce ba a san asalin cutar ba, kuma zuwa yanzu mutane 4 sun rasu sakamakon cutar kamar yadda daily trust ta bayyana. 
Darakta Janar na hukumar, Dr. Jide Idris ya ce zuwa yanzu, an ana zargin mutane 164 ne suka kamu da baƙuwar cutar. 
Dr. Jide Idris ya kara da cewa: "Mafi yawan masu kamuwa da cutar yara ne daga shekara 4-13, da kuma wasu manya. 
Marasa lafiyar sun zo daga mazaɓu daban-daban na ƙaramar hukumar." 
Ana zargin an samu mutane ɗauke da baƙuwar cutar a ƙaramar hukumar Isa. 
A cewar hukumar NCDC, mutane 22 daga mazaɓar Bargaja, da mutane 17 mazaɓar Isa ta Arewa, sai wasu mutum 98 daga Isa ta kudu ne ake zargin sun kamu da cutar. 
Sauran mazaɓun da ake fargabar sun kamu da cutar sun fito daga mazaɓar Tozali (12), da Turba (11). 
Wasu daga alamomin sun hada da kumburin ciki, zazzaɓi, amai, da rama, kamar yadda leadership ta tabbatar. 
A cewar Darakta Janar ɗin, tuni suka ɗauki matakin kar-ta-kwana wajen shawo kan cutar tare da yin bincike. 
Ya ce sun haɗa hannu da ma'aikatar lafiya ta jihar Sakkwaton domin lalubo bakin zaren. 
Dr. Idris ya ce biyu daga wadanda ake zargi na dauke da makanciyar wannan cutar na samun kulawar kwararru a asibitin koyarwa na Usmanu Danfodiyo, UDUTH.