A cikin mutane 10 masu cutar HIV, 6 matane ----Hukumar Yaki Da Cutar Kanjamau

A cikin mutane 10 masu cutar HIV, 6 matane ----Hukumar Yaki Da Cutar Kanjamau

Darakta Janar na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta kasa, NACA, Dakta Gambo Aliyu, ya ce shida cikin 10 na masu dauke da cutar kanjamau a Najeriya mata ne.

Aliyu ya kuma ce, ƴan mata a Najeriya sun ninka maza masu daidai da shekarun su yawan masu ɗauke da cutar.

Aliyu, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya Talata don tunawa da ranar mata ta duniya ta 2024, ya yi kira da a karfafawa matan Najeriya.

Ana bikin ranar mata ta duniya ne duk ranar 8 ga Maris kowace shekara.

"Zuba hannun jari a harkokin mata ba wai kawai sadaukar da kai ba ne na kudi, jari ne don ci gaban al'ummominmu mai dorewa.

"Lokacin da muka karfafa mata, za mu haifar da wani tasiri mai canzawa wanda ke tasiri ga iyalai, al'ummomi, da kuma kasa baki daya."

Aliyu ya bayyana cewa, a taron na bana, NACA ta jaddada aniyar ta na karfafar mata da ‘yan mata, tare da lura da rawar da suke takawa wajen yaki da cutar kanjamau.