An yi Garkuwa da Sarkin Bunguɗu kan hanyar Kaduna zuwa Abuja
'Yan bindigar sun ɓarin wuta da masu tsaron Sarkin in da suka kashe mutum ɗaya kafin su samu nasarar tafiya da Sarkin.
An yi Garkuwa da Sarkin Bunguɗu kan hanyar Kaduna zuwa Abuja
Wasu majiyoyi na cewa Masu garkuwa da mutane sun sace mai Martaba Sarkin Bungudu Alhaji Alhassan Attahiru a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
'Yan bindigar sun ɓarin wuta da masu tsaron Sarkin in da suka kashe mutum ɗaya kafin su samu nasarar tafiya da Sarkin.
Har yanzu ba wani bayani kan Garkuwa da sarkin domin waɗanda suka sace shi ba su ce uffan ba.
A yau Talata ne aka yi wannan ta'adanci a lokacin da sojoji suke a jihar Zamfara suna ƙoƙarin kawar da 'yan bindigar a jihar gaba ɗaya.
managarciya