Kansiloli Sun Tsige Shugaban Karamar Hukuma a Kaduna
“Wasu daga cikin kwangilolin an biya kudaden su duka ba tare da yin aikin ba sannan wasu an yi aikin amma kasa da abin da ya kamata da wasu kuma an kara kudin aiki fiye da yadda ya kamata.

Kansiloli tara daga cikin 10 a karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna sun tsige shugaban karamar hukumar Mathias Siman daga kujerarsa bisa zargin rashin yi aikin da aka zabe sa ya rika yi.
An tsige Siman bayan kudirin da Zachariah Achi daga gundunmar Bandon ya gabatar wanda Fidelis Kukwui daga gungumar Zankang wanda ya mara wa baya da yake zargin shugaban karamar hukumar da yin almubazzaranci da sakaci a aiki.
Achi na kuma zargin shugaban karamar hukumar da bayar da kwangiloli ga kamfaninsa wanda ya saba wa doka.
“Siman ya bai wa kamfanin sa SMK Nigeria Limited manyan kwangiloli da kudinsu ya kai naira miliyan 153.
“Wasu daga cikin kwangilolin an biya kudaden su duka ba tare da yin aikin ba sannan wasu an yi aikin amma kasa da abin da ya kamata da wasu kuma an kara kudin aiki fiye da yadda ya kamata.
“Haka ya sabawa sashe na 48 na dokar kananan hukumomi ta shekarar 2018 da kuma dokar gwamnatin jihar Kaduna ta shekarar 2016.
Kakakin majalisar, Stephen Atuk, ya bayyana cewa Siman Mathias yanzu ta tabbata an tsige shi a matsayin shugaban hukumar daga ranar Talata 31 ga Oktoba 2023.
Siman ya musanta zargin da ake masa yana mai cewa an tsige shi daga kujerarsa ba tare da an sanar da shi ba sannan ba tare da an ba shi daman kare kansa ba.
Ya ce ya amince da hukuncin da majalisar da yanke.
“ Wadannan Kansiloli duk ‘yan’uwana ne kuma na bar wa Allah komai. Ba zan je kotu ba.
“Dole ne mu yi hakuri da junanmu a wannan rayuwar.