Kotu Ta Daure Mutumin da Aka Kama da Katin Zabe 101 a Sakkwato Shekara Daya  Gidan Yari 

Kotu Ta Daure Mutumin da Aka Kama da Katin Zabe 101 a Sakkwato Shekara Daya  Gidan Yari 

 

Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) tace mutumin da aka kama da Katin zaɓe 101 a Sakkwato, Nasiru Idris, Kotu ta yanke masa hukuncin zaman gida gyaran Hali na shekara ɗaya. The Caɓle ta ruwaito cewa INEC ta sanar da hukunta mutumin ne a wata sanarwa da Festus Okoye, kwamishinan hukumar na ƙasa ya fitar ranar Lahadi. 

"A wasu makonni da suka gabata, hukumar yan sanda ta kama wasu mutane bisa zargin mallakar Katunan zaɓe ba kan ƙa'ida ba a wasu jihohi."
"A ɗaya daga cikin Kes ɗin, yan sanda sun miƙa binciken da suka yi ga hukumar zaɓe, sakamakon haka Kotun Majistire a Sakkwato ta hukunta Nasiru Idris bayan kama shi da katin zaɓe 101. An yanke masa shekara ɗaya a gidan Yari."
"Haka nan yan sanda a Kano sun kama wani mutumi ɗauke da Katunan zaɓe 367. Tuni aka garfanar da wanda ake zargin gaban Ƙuliya kuma INEC na bibiyar shari'ar."
Game da batun karban katin PVC, INEC tace zata zauna da baki ɗaya kwamishinonita na jihohi a jihar Legas daga ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa ranar 3 ga watan Disamba.