"Rashin Gudanar da zaben fidda-gwani a Bede/Jakusko karan-tsaye ne ga dimukuradiyya"
Daga Sharafudeen Al-Amin, Yobe
Magoya bayan yan takarar kujerar majalisar wakilai a jam'iyyar APC da ke mazavar Bade/Jakusko a jihar Yobe, suna ci gaba da guna-gunin rashin gudanar da zaven fidda-gwani a mazavar, sama da awanni 24 da fara zaven a sauran mazabu a jihar da ma qasa baki daya, al'amarin da ke ci gaba da jawo tayar da jijiyoyin wuya tare da rashin sanin makomar siyasar yanki.
Ra'ayoyi da dama daga bakin jama'ar waxannan qananan hukumomi guda biyu; Bade da Jakusko sun shaida wa wakikinmu qorafinsu tare da tambayar neman sanin dalilan da ya sa aka qi gudanar da zaven a Government Lodge da ke garin Gashuwa, wanda nan ne cibiyar aka saba gudanar dashi a yankin, kamar yadda dokar zaven ta tanada tare da sauran yankuna a faxin qasar nan. Haka kuma, tun kimanin qarfe 7:30 na safiyar ranar Jummu'a jama'a suke dako, amma babu ko xaya daga jami'an kwamitin zaven jam'iyyar APC da aka turo daga Abuja ko na INEC da ya taka qafarsa a wajen a tsawon yinin.
Mohammed Suleiman ya na xaya daga cikin magoya bayan da ya bayyana rashin gamsuwarsu dangane da take-taken masu ruwa da tsaki a harkar zaven fidda-gwanin, alhalin an gudanar da zaven a sauran yankuna guda shidda (6) da ke jihar, savanin mazavar Bade/Jakusko, wanda har lokacin rubuta wannan rahoton (ranar Lahadi) ba a gudanar dashi ba.
"Sannan abin da ya xaure mana kai shi ne, yanzu haka ana gudanar da zaven fidda-gwani na Sanatan yankin, amma uwar jam'iyyar APC taqi tace uffan dangane da qin gudanar da na majalisar wakilai a wannan mazava tamu."
"Har wala yau, abin zargi ne idan dai har za a gudanar da zaven a yankin da yake fuskantar matsalar tsaro amma ayi kunnen uwar-shegu da na yankinmu."
"Amma mun samu labarin wai an tura zaven zuwa Damaturu, fadar jihar Yobe, amma duk da hakan babu abin da aka gudanar a can xin ma."
Mohammed ya yi zargin cewa bisa wasu voyayyun bayanan da ake nuqu-nuqu dasu sun nuna ana qoqarin karkata akalar takarar ga wani shafaffe da mai, wanda wasu manya ke son a ba.
Wakilinmu ya tuntuvi yan takarar, domin jin ra'ayoyinsu, wanda Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya bayyana cewa, sun yi duk shiri da tsarin da doka ta tanada kan zaven amma har yanzu basu san me yake faruwa ba, face sai rufa-rufa ake musu; ba a fito fili qarara ba wajen gaya musu dalilin da ya sa ba a gudanar da zaven ba.
Kaitafi ya ce, "Tun ranar Jummu'a da aka tsara gudanar da zaben muke jiran jami'an zaben, amma shuru, amma daga baya mun samu labarin an kwashe delegates din Bade da Jakusko zuwa Damaturu. Hakan yasa na kira jami'an zaben don su yi mana bayanin yaushe za a gudanar da zaben? Shi ne suka ce har sun kamo hanya, sun kusa Potiskum aka ce wai su dawo Damaturu, shi ne na ce wa ya ce ku dawo? Sai suka ce umurni ne daga sama."
"Daga baya shima aka umurci shugaban qaramar hukumar Jakusko ya tafi Damaturu, wai can za a yi zaben. Amma nayi mamakin me ya hada Damaturu da zaben majalisar wakilai (House of Representative)? Alhalin dokar zabe ta ce a Gashua za a yi shi. A haka na wuni a ranar jummu'a, sai kimanin 8:00pm na fita zuwa Damaturu. Ina zuwa na tarar da Ya'u Galadima, Mohammed Karage da Madaki Manu Girgir a Presential Lodge, muka gaisa kuma na tambayi jami'an zaben cewa me ya sa ba a gudanar mana da zabe ba? Shi suka ce na bari za a yi magana, amma shuru babu cikakken bayani."
"Amma da na binciki shugaban kwamitin zaven da aka turo daga Abuja, Mallam Umar Kareto, shi ne sai ya tabbatar min cewa nayi hakuri gobe (Asabar) za a zo haxa na mazavar Bade/Jakusko da zaben Sanatan Arewacin Yobe."
"Shi ne muka sake dawowa Gashua, muka sake tattara delegates don su zama cikin shiri, tsammaninmu idan an gama na Sanatan za a yi na wakilai, amma shuru babu labari, sai daga baya muka samu kishin-kishin cewa wai an ba Ya'u Galadima takara a Damaturu, kuma wai sakataren jam'iyyar APC ya ce a tafi Damaturu da DSS, Police, jami'an INEC tare da party chairman na Bade da Jakusko."
"Hakan ya sa muka zura musu idanu, kuma daga nan bamu san me yake faruwa ba, duk wanda muka kira sai ya ce bai san me yake faruwa ba. Sannan mun so ace sun fito fili sun shaida mana cewa 'Kai Sani ba ma son ka yi takarar nan'. Duk da akwai maganar da naji a wata majiya cewa an kirasu ne daga sama cewa kar a bani takara. Shi ne sai jami'an suka gaya wa shi wancan babban mutum cewa su bari ayi zaben, shi ne ya gaya musu cewa ai kowane zabe za a yi Sani ne zai ci, saboda haka kar ma ayi zaven."
Wakilinmu ya nemi tambaye shi cewa wane mataki zai xauka idan abin ya ci gaba da kasancewa a haka? Shi ne sai ya ce, "Ai xaukar matakin ba nawa bane ni kadai, sai mun zauna da sauran yan takarar, saboda yanzu haka zancen da ake suna Damaturu."
Ya qara da cewa, "Amma ta bangarena, yau zan kira uwar jam'iyyar APC don suyi mana cikakken bayani dangane da dalilan da suka saka ba a gudanar mana da zaven ba, saboda gashi lokacin zaben fidda-gwani ya wuce, daga nan sai na kama gabana. Kuma ni da jama'ata zamu zauna wuri guda domin daukar matakin bai-daya, amma ni kadai ba zan dauki wani mataki ba. Zamu zauna mu san abin da zamu yi."
A nashi vangaren, mun nemi jin ta bakin Hon. Zakari Ya'u Galadima ta hanyar wayar tafi-da-gidanka, a matsayinsa wanda shi ne Dan majalisa mai wakiltar yankin, kuma xaya daga cikin yan takarar, inda ya kada baki ya ce, ya na jiran abin da uwar jam'iyyar za ta ce kan lamarin, amma ba zai iya cewa komai ba kan al'amarin.
Shi kuma Mohammed Manu Girgir xaya dan takarar, ya nuna cewa babu wani zaven da aka gudanar a mazavar, wanda faxar hakan ke da wuya ya katse kiran, wanda na sake kiransa amma yaqi ya daga.
Har wala yau, duk qoqarin jin ta bakin shugaban jam'iyyar APC a jihar Yobe, Muhammad Gadaka tare da Sakataren sa, Abubakar Bakabe abin ya faskara; babu xaga kira ballantana mayar da jawabin saqon kar-ta-kwana da na tura musu.
A hannu guda kuma, jami'in hulxa da jama'a na jam'iyyar APC a jihar Yobe, Bakura Jibrin ya ce zancen ya zarta mafidda-gwanin ya ce wani abu a kai.
managarciya