'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane fiye da 60 a Zamfara
'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane fiye da 60 a Zamfara
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne a jiya Juma'a sun mamaye garin Rini da ke karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da mutane sama da 60.
An samu labarin cewa 'yan bindigar sun isa garin da misalin karfe 2:30 na dare inda suka yi ta harbe harbe ba kakkautawa a cikin garin na Rini.
Wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta saboda dalilan tsaro ta ce duk da cewa mazauna garin sun ki fitowa daga gidajensu duk da harbin bindiga, amma 'yan bindigar sun yi nasarar sace sama da mutane 70 a garin.
“Lokacin da suka zo, sun kai hare -hare a unguwa uku dake cikin garin da farko, a Sabon Gari, daga nan suka koma Makarantar Boko sannan daga baya suka koma tsakiyar garin Rini, ”inji majiyar.
Majiyar ta ci gaba da cewa jami'an tsaron ba su je garin ba duk da kiran da 'yan garin suka yi ta yi, inda ta kara da cewa motoci biyu kirar Hilux, dauke da sojoji daga baya sun zo garin kuma sun tafi bayan sun kwashe wasu awanni.
Kamar yanda jaridar Thunder Blowers ta ruwaito, Kakakin rundunar ‘yan sandan Zamfara, SP Shehu Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ba da adadin wadanda aka sace a matsayin 60.
Muhammad ya ce rundunar ‘yan sandan ta tura isassun jami’an tsaro don kubutar da wadanda aka sace.
managarciya