An Tsige Shugaban Ƙungiyar Masu Noman Albasa Na Jihar Kaduna

An Tsige Shugaban Ƙungiyar Masu Noman Albasa Na Jihar Kaduna

Daga Awwal Umar Kontagora, a Kaduna.
Kwamitin gudanarwa ta ƙungiyar masu noma da sarrafa albasa ta ƙasa ta dakatar da shugabanta na jihar Kaduna Alhaji Ismail Kargi daga muƙaminsa.
Sanarwar ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar na ƙasa Alhaji Aliyu Binji
Da yake bayani akan dalilan dakatarwar, yace kwanakin baya wasu daga cikin ƴaƴan ƙungiyar sun kawowa uwar ƙungiyar ta ƙasa kan dakatar da shugaban mata na ƙungiyar ta jiha, Hajiya Hauwa'u Ibrahim Zariya da Alhaji Isma'il Kargi yayi bisa wasu dalilai  na ƙashin kansa.
Hakan yasa uwar ƙungiya na ƙasa ta dauki matakin kiran ɓangarorin biyun don jin ta bakinsu don yin sulhu a tsakaninsu ƙarƙashin jagorancin shugaba na ƙasa.
Wannan taron sulhun ya gudana ne a jihar kaduna a madadin ƙungiyar ta ƙasa baki ɗaya.
Yayin zaman taron sulhun ne a Kaduna, sakataren ƙungiyar na jihar Kaduna ya fice daga zaman sulhun, wanda hakan kusan nuna rashin ɗa'a da biyayya wanda shi ma shugaban ƙungiyar Alhaji Isma'ika Kargi ya bi shi tare da umurtar mambobin ƙungiyar su fice daga zaman sulhun, a cewar ƙungiyar wannan ɗabi'ar ya saɓawa dokokin ƙungiya, dan yaci mutuncin shugabannin ƙasa da suka zo sulhun.
Kan haka uwar ƙungiya ta ƙasa, tayi zama inda ta ɗauki matakin tsige shugaban na jihar Kaduna ba tare da ɓata lokaci ba.
Uwar ƙungiyar ta bayyana cewar ta tsige Alhaji Isma'ila Kargi daga jagorancin ƙungiyar masu noman albasa da sarrafa a jihar Kaduna baki ɗaya.
Ƙungiyar tayi kira ga gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da cibiyoyin ƙasa da kar su sake yin wata mu'amala da shi da sunan shugaban ƙungiyar masu noman albasa da sarrafa shi har abinda Allah yayi.
Ƙoƙarin jin ta bakin Alhaji Isma'ila Kargi ya citura. Zuwa haɗa rahoton da daman ƴaƴan ƙungiyar a yankunan ƙananan hukumomin jihar sun yi murna da matakin ƙungiyar ta ƙasa.