Sakkwato da Wasu  Jihohin Arewa da Aka Fi Yawan Sace Mutane cikin Shekara 1

Sakkwato da Wasu  Jihohin Arewa da Aka Fi Yawan Sace Mutane cikin Shekara 1

 
Jihohin Arewa musamman a bangaren Yammaci suna fama da matsalolin ta'addanci da kuma garkuwa da mutane da ya yi katutu.
 Jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara su ne kan gaba wurin fama da matsalar wadanda dukansu ke Arewa maso Yamma. 
Rahoton SM Violence Tracker da Legit ta samu ya tabbatar da cewa an sace mutane 7,568 cikin shekara 1 a kasar a lokuta 1,130 daban-daban. 
Premium Times ta ruwaito cewa akalla N1bn ne aka biya na kudin fansa ga 'yan ta'adda a cikin shekara daga watan Yulin 2023 zuwa Yunin 2024. 
1. Jihar Zamfara Jihar Zamfara ce kan gaba inda aka yi garkuwa da mutane akalla har sau 132 wanda ya yi sanadin sace mutane 1,639. 
2. Jihar Kaduna Kaduna ta zamo ta biyu inda aka sace jama'a sau 113 wanda yawan mutane da aka sacen ya kai 1,113. 
3. Jihar Katsina Jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma ita ce ta uku inda aka sace mutane 887 a lokuta akalla 119. 
4.Jihar Borno A Borno da ke Arewa maso Gabas wacce ke fama matsalar Boko Haram, an sace mutane 720 a lokuta daban-daban har 63. 
5. Jihar Niger Niger da ke yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya ita ta kasance ta biyar inda aka sace mutane sau 48 da ya yi sanadin garkuwa da mutane 689. 
6. Jihar Sokoto Sokoto ta kansace ta shida wacce ke Arewa maso Yamma inda aka sace mutane 487 a lokuta har sau 67. 
 
Sauraren wuraren da ake sace mutanen Arewa Sauran sun hada da birnin Tarayya Abuja da aka sace mutane 404 sai Benue da mutane 186 sai kuma Kogi da aka sace mutane 170. 
Har ila yau, akwai jihar Taraba da mutane 167 sai Bauchi da mutane 114 da kuma Nassarawa da mutane 113. 
Garuruwan Arewa masu saukin garkuwa da mutane Jihohin Arewa da ba a samu matsala sosai ba su ne Gombe inda aka sace mutane biyu a lokaci daya sai Kano da aka sace mutane biyu a lokuta sau hudu. 
Sai kuma jihar Jigawa da mutane 2 a lokuta biyu da Yobe mai mutane tara a lokuta takwas sai kuma Adamawa mai mutane 11 a lokuta har sau 13. 
Akwai Plateau da aka sace mutane 26 a lokuta 24 da Kebbi mai mutane 26 a lokuta 10 sai kuma ta karshe Kwara mai mutane 80 a lokuta daban-daban har sau 27.