Dan Majlisar Tarayya  Ya Kaddamar Da Shirin Taimakon Al'ummarsa Domin Dogaro Dakai a Sakkwato

Dan Majlisar Tarayya  Ya Kaddamar Da Shirin Taimakon Al'ummarsa Domin Dogaro Dakai a Sakkwato

 
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.
 
A Sakkwato, Dan Majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumonin Dange Shuni Bodinga da Tureta a Jihar,
"font-family: times new roman, serif; font-size: large;">Ya rabawa Al'ummar mazabarsa Kayan Tallafin Sana'a   a kokarin da wasu 'yan siyasa ke yi na Tallafawa Alummar su da kayan more rayuwa da dogaro da kai.      
Dan Majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin,
ya rabawa Al'ummar mazabarsa kayan tallafin Sana'a, da suka  hada da mashuna Masu Taya ukku, na'urorin sanyaya ruwa, Babura, injimukkan ban ruwa   janareto da kayan sana'ar Mata, matasa,  da sauran su. 

Rabon tallafin da aka yi karshen mako, a  a harabar hidikwatar karamar hukumar mulkin Dange Shuni ya Sami halartar manyan Mutane daga bangarori daban daban a fadin jihar.
Da yake jawabi a Lokacin bukin Dan Majalisar
 Dakta Shehu Balarabe Kakale  ya janyo hankalin al'umma na sanin tarihin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da irin gudunmawar da ya basuwa dangane da abin da ya shafi Sha'anin kasuwanci domin dogaro dakai 'wanda tun farko kafin shigowar turawan mulkin mallaka/ turawan yamma, sun same mu  da tsare tsaren mu na  abin da ya shafi mulki, kasuwanci da dai sauransu' shi ne ya ga dacewar a kirkiro wannan Shirin SHIRIN FARFADO DA TATTALIN ARZIKI, MASANA'ANTU DA SAMAR WA MATASA DA MATA SANA'O'I NA DOGARO DA KAI, MAI TAKEN
"BABBAN TSARIN RAYA MASANA'ANTU DA SANA'O'I NA SARKIN MUSULMI MUHAMMADU BELLO".
  
Dan Majalisar ya bayyana cewa bisa la'akari da yadda zamantakewa take tun tsawon lokaci na Amfani da sunayen Sana'oi da Sunan unguwa misali irin su majema makera, masaka, madunka, da mallamawa da makamantan su, ya ga dacewar a zakulo irin wadannan Masu sana'oin domin tallafa musu.
A saboda haka ya janyo hankalin wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi kamar yadda yadda ya kamata.

Shi ma a jawabin sa Gwamnan Jihar Sokoto Wanda Dan takarar kujerar Gwamnan Jihar, a jamiyyar PDP , Hon. Malam Sa'idu Umar Ubandoma ya wakilta,
Ya godewa Dan Majalisar akan wanna hubbasar da yayi na samarwa Al'ummar mazabarsa wadannan kayan Tallafi,
A saboda haka ya shawarce su da su yi amfani da su kamar yadda ya kamata.
Haka ma ya janyo hankalin sauran masu rike da mukami irin nasa dasu koyi Dan Majalisar Domin tallafawa Al'ummar mazabarsu Domin samun abin dogaro dakai.  
A nasa jawabin, Shugaban hukumar Zakka na Sokoto, Sadaukin Sakkwato malam Muhammad Lawal Maidoki ya bayyana alakar hukumar da dan majalisar "muna ayukkan alkhairi da Honarabul Kakale tun yana Kwamishina".  
Ya kuma yi kira ga gwamnatoci da su takawa wasu masu son rushe Da'awar Dan fodiyo birki. 

Taron ya samu halartar wakilin sarkin Musulmi, da sauran Shugabannin na Siyasa, Alummah da sauran su. 
Ko a watannin baya Dan majalisar yayi irin wannan rabon kayan ga dinbin Al'ummar yankin sa, kuma cikin sati mai zuwa zai kaddamar da wasu motoci da ya samar ga kananin hukumomi ukku na yankin sa a wani shiri na hadaka da Hukumar zakka na wakafin lafiya.