Gwamnatin Katsina Za Ta Kafa Hukumar Zakka Da Wakafi, Bayan Alwashin Gina Gidajen Marayu
GWAMNATIN JIHAR KATSINA, ZATA KAFA HUKUMAR ZAKKA DA WAQAFI, TA KUMA SHA ALWASHIN BAYAR DA GUDUNMUWA GA GINA GIDAJEN MARAYU DA YAN GUDUN HIJIRA
Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.
A kokarin da Gwamnatoci ke yi na ganin sun Samar da hanyoyin bunkasa Tattalin Arzikin jihohin su da Kuma sanarwa Alummar su Abubuwan more rayuwa da taimakawa mabukata, musamman Marayu, zawarawa,tsofaffi da sauran maras galihu , Gwamnatin jihar katsina, ta bi sahun jihohin na ganin ta kafa Hukumar karba da raba Zakka da wakafi kamar ta jihar Sokoto watau Zakka da Wakafi A Jihar Sokoto ,da jihohin Zamfara da sauran su, dadin dadawa Gwamnan ya tabbatarwa katsina wannan abin Alkhairi da ke tafe, inda
Gwamnan jihar katsina,ya bayyana cewa ya kaddamar da aza harsashin gina gidajen Marayu guda (400) tare da bada gudunmuwa ta milyoyin Naira.
A ranar Lahadi 30/07/2023, Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Dr. Dikko Umar Radda ya jagoranci aza harsashin ginin gidajen guda 400, Asibiti, Masallaci da kuma wurin koyon sana'o'i ga Marayu da Yan Gudun Hijira a sabuwar unguwar Dandagoro dake cikin Karamar hukumar Batagarawa, jihar Katsina.
Da yake gabatar da jawabin shi Jim kadan kafin kaddamar da aikin Malam Dikko Radda ya yaba tare da godema daukacin al'umma da sukai wannan tunani na ganin an gudanar da wannan aiki.
Gwamnan ya Kara da cewa" Al'umma su dage wajen zuba jari wanda zasu samu sakamakon gobe kiyama, ya Kuma ja hankali su dasu dage wajen Shiga cikin irin wannan Ayukkan Domin Ciyar da al'umma gaba masanman masu karamin karfi.
Daga karshe, ya bayyana gudunmuwa ta zunzurutun kudi har Naira milyan dari na gwamnati jihar katsina da kananan hukumomin, tare da ta milyan biyar ta kashim kansa da Kuma ta Naira milyan goma ta hamshakin Dan kasuwar nan na jihar katsina Alh. Dahiru Mangal.
Shima a nashi jawabin maraba shugaban kungiyar zakka da wakafi ta katsina Dr. Ahmad Musa Filin Samji ya bayyana yadda aikin na gina gidajen da wuraren zai kasance.
Inda ya bayyana cewa" an yi shiri na inganta rayuwar wadanda za su zauna a gidajen ta hanyar samar da gonar dabino da sauran itatutwan alfarma da kuma yadda al'umma za su sanya hannun jarinsu a wannan gona ta hanyar wakafi.
Daga karshe ya godema gwamnan jihar katsina tare da sauran al'umma akan gudunmuwar da suka bada na ganin wannan aiki wanda zai lakume sama da Naira milyan dubu daya ya gudana a cikin nasara.
Mutane da dama nesuka tofa albarkacin bakin su daga ciki akwai wakilin Sadaukin Sakkwato (Engr. Mal. Muhammad Lawal Maidoki) Shugaban Zakka da Wakafi ta jihar Sokoto, kana Shugaban kungiyar Zakka na Kasa, Wanda sakataren shi Dr. Aliyu Muhammad Tahir ya wakilta, Wakilan sarakunan katsina da Daura, malamai tare da masu ruwa da tsaki.
Taron wanda ya gudana a harabar inda za'a Gina gidajen ya samu halartar shugaban ma'aikata na gidan gwamnati jihar katsina Hon. Jabiru Salisu Abdullahi ,wasu daga cikin shugabanin kananan hukumomi na jihar katsina, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Hon. Aliyu Albaba masu baiwa gwamnan jihar katsina shawara na musanman, Mata da maza da sauran al'umma.
Wata takardar da aka rabawa manema labarai wadda CPS Ibrahim Kaula Muhammad ya sakawa hannu, ta bayyana cewa Bada jimawa ba , Gwamnatin jihar zata aikawa Majalisar Dokokin jihar dokar kafa Hukumar Zakka da wakafi ,kamar yadda doka ta tanada.
Masana sun tabbatar da idan Daukacin Gwamnonin Arewa cin kasar nan da sauran gwamnoni suka kafa Hukumar suka bata goyon baya, su Kuma masu Hali suka dinka Bada zakkar su ko Wakafi to lalle zaayi ban kwana da talauci da kuncin Rayuwar da tayi katutu a Arewacin kasar nan da sauran sassan kasar nan.
managarciya