Lamido Ya Yi Ta’aziyar Rasuwar Danmadamin Isa
Dan takarar Sanata a yankin Sakkkwato ta Gabas cikin jam’iyar APC Alhaji Ibrahim Lamido ya mika ta’aziyar rasuwar Kwamishinan harkokin addini a jihar Sakkwato Alhaji Usman Suleiman Danmadamin Isa ga iyalansa da mutanen karamar hukumar Isa da jihar Sakkwato baki daya.
Ibrahim Lamido a bayanin da ofishin yada labaransa ya fitar a yau Assabar ya bayyana cewa rashi ne babba mutanen jiha suka yi a ranar Jumu’a, wanda zai yi wuyar a cike gibin rashinsa.
Ya ce ana rasa mutumin kirki mai aiki tukuru da son al’ummarsa ga shi kuma mutum ne mai kyauta da sakin fuska.
Lamido ya mika sakon ta’aziyarsa ga mata da ‘ya’ya da dangin margayin, Allah ya gafarta masa ya yi masa rahama ya sanya mutuwa hutu gare shi.
managarciya