Buhari Ya Soke Hukumomin Man Fetur  DPR Da PPPRA Da PEF A Najeriya

An kafa wasu sabbin hukumomi biyu da za su maye gurbinsu, wato Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority da Nigerian Upstream Regulatory Commission, kuma hukumomin biyu za su sa ido ne kan hakar mai da sarrafa shi a Najeriya. Ƙaramin ministan harkokin man fetur, Timipre Sylva ya tabbatar da kafa sabbin hukumomin da fara aikinsu kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Buhari Ya Soke Hukumomin Man Fetur  DPR Da PPPRA Da PEF A Najeriya

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta soke hukumomi uku a ɓangaren mai kamar yadda sabuwar dokar man fetur ta tanada.

Dokar, wadda aka sa hannu a kanta a watan Agusta ta buƙaci a soke hukumomin DPR da PPPRA da PEF.

An kafa wasu sabbin hukumomi biyu da za su maye gurbinsu, wato Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority da Nigerian Upstream Regulatory Commission, kuma hukumomin biyu za su sa ido ne kan hakar mai da sarrafa shi a Najeriya.

Ƙaramin ministan harkokin man fetur, Timipre Sylva ya tabbatar da kafa sabbin hukumomin da fara aikinsu kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya ƙaddamar da hukumar darektocin sabbin hukumomin a Abuja ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta kare ayyukan ma'aikatan tsoffin hukumomin uku da aka soke duk da cewa an sallami shugabanninsu daga mukamansu.