An kashe mutum 1 An jikkata 18 yayin faɗa tsakanin 'yan APC da PDP a Zamfara
A yau Lahadi, rundunar ƴan sanda a garin Gusau na jihar Zamfara ta tabbatar da kashe mutum daya, tare da jikkata wasu 18 a wata arangama da wasu ƴan bangar siyasa suka yi.
Rundunar ƴan sandan ta ce ana zargin ƴan jam'iyyun APC da PDP ne su ka yi gadan a jihar.
Kakakin rundunar, Muhammad Shehu ne ya tabbatar da hakan a wani sakon kar-ta-kwana da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na ƙasa a Gusau a yau Lahadi.
Shehu, wanda ya tabbatar da cewa rundunar ta samu rahoton kisan, ya ce: "An fara bincike mai zurfi kan lamarin da nufin tabbatar da cewa wadanda suka aikata laifin sun fuskanci fushin doka."
Sai dai kakakin ya ki yin karin haske kan lamarin.
Tabbatarwar ta Shehu ta biyo bayan zargin da jam’iyyar APC ta yi na cewa wasu ƴan barandan siyasa na PDP ne ta dauka hayar su su ka kai hari tare da kashe mutum daya da raunata wasu 18 ba tare da dalili ba.
Zargin na APC na kunshe ne a wata sanarwa da Yusuf Idris, sakataren yada labaran jam’iyyar a Gusau ya fitar a jiya Asabar Asabar.
managarciya