Jam'iyar PDP Ta Dakatar Da Sanannun 'Yan Siyasa 7 A Jihar Kebbi 

Jam'iyar PDP Ta Dakatar Da Sanannun 'Yan Siyasa 7 A Jihar Kebbi 
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache
 
Jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ta  kori jiga-jiganta 7 bisa zargin yiwa jam'iyyar zagon kasa a cewar sanarwar da aka fitar aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
Takardar wadda Sakataren jam'iya Abubakar Bawa Kalgo ya sanyawa hannu ya ce suna sanarwa mutanen gari da magoya bayan PDP sun dakatar da mutanen har sai baba ta gani.
 
Alamu na cigaba da nuna cewa wankin hulla yana neman ya kai jam'iyyar PDP rana a jihar Kebbi a dai-dai lokacin da ake cigaba da tunkarar zaben gwamnoni da yan majalisu.
 
PDP ta shiga rudani a Kebbi inda uwar jam'iyyar ta bada wata sanarwa ga manema labarai kan korar jiga-jiganta 7 daga jam'iyyar bisa zargin su da yiwa jam'iyyar zagon kasa.
 
Akwai badakala kan rikicin jam'iyyar adawa ta PDP wanda ya kwashe shekaru ana cece-kuce kawo yanzu ba'a samu dai-dai to tsakanin manyam jiga-jigan ba an rasa zaune an rasa tsaye.
Mutanen su ne Kabiru Tanimu SAN da Haruna Sa'idu Dan D. O da Sani Bawa Argungu da Ibrahim Abdullahi Manga da Buhari Bala da Bala Abdullahi da Maryam Isa