Buhari Bai Goyi Bayan Kowane Ɓangare Ba  A Siyasar Kano----Garba Shehu

Buhari Bai Goyi Bayan Kowane Ɓangare Ba  A Siyasar Kano----Garba Shehu
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce shi ba ya goyon bayan kowanne ɓangare a rikicin jam'iya mai mulki ta APC a Jihar Kano.
A jiya Asabar ne dai Shugaban APC, ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau, Ahmadu Haruna Ɗanzago ya shaidawa BBC Hausa cewa Buhari ya taya shi murnar zama shugaban jami'ya a Kano a ganawar da ya yi da shugaban a fadarsa a ranar Juma'a.
Sai dai kuma, a wani martani na gaggawa, Buhari ya ce shi bai goyi bayan ko wanne ɓangare a rikicin ba.
A wata gajeruwar sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan yaɗa Labarai, Garba Shehu ya fitar a jiya Asabar, fadar shugaban ƙasa ta ce, "wannan ba gaskiya ba ne. Wannan ba zai taɓa faruwa ba yayin da magana ta ke gaban kotu.
"A gaskiya Shugaba Buhari bai goyi bayan ko wanne ɓangare ba.
"Shi dai ya na goyon bayan APC a matsayin ta na jam'iya, yadda za ta zama mai ƙarfi da haɗin kai, ba wai wani ɓangare ba," inji Garba Shehu.
Hakan ke nuna shugaba Buhari ya zuba masu ido kenan duk wanda yafi ƙarfi ya murƙushe ɗayan.
Yakamata Buhari ya warware matsalar da kansa ba wai ya sa musu ido ba tun da shi babba ne jam'iyar.