Ambaliya: Ɗongote ya ba da tallafin biliyan 1.5 Don tallafawa mutanen Borno

Ambaliya: Ɗongote ya ba da tallafin biliyan 1.5 Don tallafawa mutanen Borno

Ambaliyar Maiduguri: Dangote ya bada gudunmawar Naira biliyan 1.5 ga NEMA da gwamnatin Borno 

Hamshaƙin attajirin Afirka,  Aliko Dangote ya ce ya bayar da tallafin Naira biliyan ɗaya ga Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, da kuma Naira Miliyan 500 ga gwamnatin jihar Borno.

BBC Hausa ta rawaito cewa Dangote ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jaje da ya kai Maiduguri a yau Juma'a.