Rundunar 'Yan Sanda Ta Sha Alwashin Ceto Dukkanin Mutanen da ke Hannun 'yan bindiga

Rundunar 'Yan Sanda Ta Sha Alwashin Ceto Dukkanin Mutanen da ke Hannun 'yan bindiga

 

Rundunar 'yan sandan kasar nan ta sake daukar alkawarin ceto dukkanin mutanen da miyagu su ka sace a sassan Najeriya. 

Babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ne ya sha alwashin a lokacin da ya ke yabawa jami'ansa kan jajircewarsu wajen ceto likitoci dalibai 20 daga hannun miyagu. 
Channels Television ta wallafa cewa babban Sufeton ya ce daga yanzu ba za su huta ba, har sai an tabbatar da kwato mutanen da ke tsare a maboyar miyagu. 
Ya bukaci hadin kai daidaikun jama'a da kungiyoyi wajen ganin an cimma manufar kakkabe rashin tsaro.
Rundunar 'yan sandan kasar nan ta bayyana muhimmancin samun hadin kan jama'a wajen raba kasar nan da ayyukan ta'addanci, Jaridar Punch ta wallafa labarin. 
Babban Sufeton 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya kuma shawarci jama'a su rika shiga al'amuran tsaro domin tabbatar da tsare rayukansu 
Rundunar 'yan sanda ta yaba da jajircewar ofishin mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro (NSA), wajen dakile ayyukan ta'addanci a kasar nan. 
Babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ya ce ofishin NSA na ba su hadin kai wajen tabbatar da ya sauke nauyin tsaron rayukan jama'a da ya rataya a wuyansa. 
A baya kun ji cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta ce ba ta da labarin miyagu sun kai hari Gobir, tare da sace mutane sama da 150 kwanaki kadan bayan kashe sarkin garin. Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa'i ne ya bayyana haka, amma ya tabbatar da cewa yankin Gobir na fuskantar barazanar tsaro.