Abin da 'yan majalisar waƙillai suka yi bayan rasuwar mutane 77 a jihar Neja

Abin da 'yan majalisar waƙillai suka yi bayan rasuwar mutane 77 a jihar Neja

Tawagar 'yan majalisun dokokin Najeriya sun jajantawa gwamnatin jihar Naje bisa iftila'in gobarar tankar mai da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 77 a jihar.

Yan majalisun sun yi ta'aziyar wadanda suka rasa rayukansu da dukiyoyin su inda suka mika sakon ta'aziyarsu ga gwamnan jihar Naje Umaru Muhammad Bago.

Tawagar ta hada da Hon Muktar Aliyu Betara Biu/Bayo Shani Kwaya Kusar  Borno Hon Kabir Ibrahim Tukura Zuru Fakai Danko Wasagu Sakaba Kebbi Hon Dujima Adamawa Ltd. Musa Haliru.

Tawagar ta kuma yi kira ga al'ummar jihar da ta rika taka tsantsa wajen daukar matakan kariya domin kare afkuwar gobarar da sauran bala'o'i anan gaba.

Daga Abbakar Aleeyu Anache