Rashin Albashi: Ma'aikatan Filato Sun Shiga Yajin Aikn Sai Baba-ta-gani

Rashin Albashi: Ma'aikatan Filato Sun Shiga Yajin Aikn Sai Baba-ta-gani

Rashin Albashi: Ma'aikatan Filato Sun Shiga Yajin Aikn Sai Baba-ta-gani

Ma'aikatan jiar Filato sun tsunduma a cikin wani yajin aiki sai baba-ta-gani bayan da gwamnatin jihar ta kasa cimma bukatunsu.

Matakin shiga yajin aikin na kunshe ne cikin matsayar da kwamitin sasantawa na jihar Filato waton Joint Negotiation Council ya cimma a ranar Laraba da dare,

Matsayar na cikin takardar da shugaba Titus Malau da Sakatare Timothy Gopep suka sanyawa hannu bayan kammala wa'adin kwana hudu da suka baiwa gwamnati.

Shugabanin bayan sun yi zama da Sakataren gwamnati da shugaban ma'aikata sun ce lamarin a bayane ya nuna gwamnati ba da gaske take na biyan bukatun ma'aikatan Filato kafin wa'adinsu ya kare a 29 ga watan mayu ba.

Bayan zama da kungiyar kwadago NLC da TUC shugabanni sun aminta da shiga yajin aiki har illa Masha Allah, sai ko in gwamnati ta cika alkawalinta a kasa.

 Kan haka sun roki dukan ma'aikata su ba da hadin kai har gwamnati ta cika alkawalinta.

Managarciya ta fahimci ma'aikatan na rigima da gwamnati ne kan kin biyan albashi da sauran hakki da aka kasa biya.