Ƴansanda sun fake da barazanar tsaro ne kawai don su hana Maulidin Tijjaniyya - Gwamnatin Kano 

Ƴansanda sun fake da barazanar tsaro ne kawai don su hana Maulidin Tijjaniyya - Gwamnatin Kano 

Gwamnatin Jihar Kano ta zargi ƴasanda da kokarin hana taron addini na na dariƙar Tijjaniyya na shekara-shekara a jihar, inda ta ƙaryata cewa akwai barazanar tsaro a jihar kamar yadda rundunar ƴansanda ta sanar a yau a jihar.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a Fadar Sarkin Kano a yau Juma’a, Kwamishinan yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya musanta gargadin da ‘yan sanda suka fitar tun da fari.

Waiya ya ce rundunar ƴansanda kawai ta fake da barazanar tsaro ne don ta hana gudanar da taron Mauludin na Tijjaniyya na kasa, wanda ya ce an kwashe kisan shekaru 40 ana gudanar da shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa, duk da matakin da ƴansanda suka dauka, Mauludin zai gudana  kamar yadda aka tsara a filin wasa na Kofar Mata, yana mai tabbatar wa wadanda ke son halarta cewa gwamnatin jihar ba za ta bari a samu wata matsala ba.