Ba za mu sasanta da ƴan ta'adda ba - Gwamnatin Katsina 

Ba za mu sasanta da ƴan ta'adda ba - Gwamnatin Katsina 

Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaryata rahoton cewa ta na sansanta wa da ƴan fashin jeji, sakamakon rahoton cewa ta na sasanta wa da ƴan fashin jeji a karamar hukumar Batsari.

Da ya ke zantawa ta wayar tarho da wakilin DAILY TRUST, Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar Katsina, Dakta Bala Salisu, ya ce gwamnatin jihar na nan a kan bakar ta na kin tattaunawa da yan ta'adda.

Sai dai kuma ya ce hannun gwamnatin a bude ya ke don ta karbi duk wani ɗan ta'adda da ya ajiye makamai ya runugmi zaman lafiya.