Matsalar Tsaro: Kungiyar Musulunci Ta Shirya Addu'ar Samun Zaman Lafiya A Sakkwato

Matsalar Tsaro: Kungiyar Musulunci Ta Shirya Addu'ar Samun Zaman Lafiya A Sakkwato

 

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto .

 

 

 Sarkin Musulmi kana Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunchi A Nigeria, Alhaji .Muhammad Sa'ad Abubakar  ya Jagorancin Addu'oin Neman Zaman Lafiya A Arewancin Kasar Nan Da Nageria Gaba Daya.

A Wajen taron angabatar da kasida mai taken 'Muhimmancin Zaman Lafiya da Hanyoyin Tabbatar da Shi' Wanda babban  Limamin Masallacin jimua na Sarkin Musulmi Muhammad Maccido, Dr. Muhammad Sani Dan Gwaggo ya gabatar, tare da Sharhi da ga Sheikh Aminu Abdullahi Sufi, Imam S.P Abdullahi Mukhtar da sajan Imam Isa Umar ya wakilta, da Malam Usman bn Ali da sauran su.

An Gudanar da Addu'oin ne A Masallacin Mujaddadi Shehu Usumanu bn Fodiyo ( T.B ) dake Sokoto.

Malamman Dasu Kayi Addu'oi Sun Hada da Sarkin Malamman Sakkwato, Limamin Masallacin Sarkin Musulmi Muhammad Bello da Liman Masallacin Shehu da Sauran Limamai da Mallamai.

Lokacin Gudanar da Addu'oin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya na tare da  Sauran Yan Majalisar sa.

Din bin Al'ummah Musulmi ne daga kungiyoyin addinin musulunci daban daban suka samu halartar taron, Wanda akayi maka mancin shi a watan da ya gabata a Masallacin Sarkin Musulmi Muhammad Bello da ke daf da fadar mai martaba sarkin Musulmi a nan cikin garin Sakkwato, 

Allah Ubangiji Ya Kawo Muna Zaman Lafiya Mai Daurewa A Kasa da Duniya baki daya