2023: Kwankwaso ya buƙaci 'yan Nijeriya da su yi nazari kan kundin manufofin mulkinsa

2023: Kwankwaso ya buƙaci 'yan Nijeriya da su yi nazari kan kundin manufofin mulkinsa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shawarci duk wadanda suka cancanci kada kuri’a a kasar nan da su samu lokaci su yi nazari kan kundin manufofin mulkinsa na neman tabbatar da shugabanci na gari.

 Kwankwaso ya bayar da shawarar ne a jiya Juma’a a Abuja, jim kadan bayan kammala sallar Juma’a a masallacin Al-Habibiyah Islamic Society’s.

Tsohon gwamnan jihar Kano da ya yi wa’adi biyu ya ce akasarin abin da ya yi niyyar yi idan aka zabe shi a matsayin shugaban Nijeriya a 2023 duk su na cikin kundin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, ya ruwaito cewa Kwankwaso, a cikin kundin mai shafuka 160 na manufofinsa mai taken “Alkawari na zuwa gare ku: Tsarin RMK2023”, ya bayyana alkawura 20 da zai cika idan aka zabe shi.

Ya yi alkawarin samar wa ‘yan Nijeriya jagoranci na kishin kasa da cancantar da za a yi amfani da su bisa ka’idojin rayuwar al’umma.

"Za mu yi adalci ga kowa kuma za mu tabbatar da gaskiya da adalci a kowane mataki na mulki," in ji Mista Kwankwaso.

A nasa bangaren, babban limamin masallacin Al-Habibiyyah, Fuad Adeyemi, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi abin da ya dace domin kasar ta daidaita.

A cewarsa, idan dukkan musulmi suka yanke shawarar yin abin da ya dace da taimakon juna, hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

“Ya kamata mu koyi taimakon juna, mu koyi taimakon juna.