Rikicin PDP: Ayu, Tambuwal da Sule Lamido Sun Gana Da Gwamnan Bauchi 

Rikicin PDP: Ayu, Tambuwal da Sule Lamido Sun Gana Da Gwamnan Bauchi 

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya isa jihar Bauchi a ranar Asabar domin ganawa da Gwamna Bala Mohammed. 

Ayu ya samu rakiyar darakta janar na kungiyar kamfen din takarar shugaban kasa na PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, PM News ta rahoto.
Tawagar sun isa Bauchi da yamma sannan suka yi wata ganawar sirri tare da mai masaukinsu, rahoton Punch. 
Da yake jawabi jim kadan bayan ganawar, Ayu ya bayyana Mohammed a matsayin daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki na kasa wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jam'iyyar. 
"Mun zo nan ne don sanar da kai wasu ci gaba da ke gudana a jam'iyyar, sannan mu ji shawararka mai cike da hikima saboda kai ba gwamnan Bauchi bane kawai, kai shugaba ne a kasar nan. 
"Kana da kwarewa a duk wuraren da kayi aiki, kuma muna bukatar mutane irinka a wannan kamfen din, daga lokaci zuwa lokaci ya zama dole mu dunga zagayoqa, mu tuntuba sannan mu sanar maka da wasu abubuwa."
Da yake martani, Mohammed ya bayyana cewa shi din dan jam'iyya ne mai biyayya kuma da yarda da ita, yana mai cewa: "Mun jingina da bangon jam'iyyar wajen zama abun da muka zama.